
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa wadanda suka rasa ƴan uwansu a hare-haren ta’addanci da aka kai a jihohin Sokoto, Kaduna da Plateau.
A cikin sakon ta’aziyyar da kakakinsa , Garba Shehu ya fitar a jiya Talata a Abuja, shugaban ya sake yin duba a kan harkar tsaro, bayan rahotannin asarar rayuka da dama a hare-haren.
Ya kuma ba da tabbacin goyon bayan gwamnatin tarayya ga jihohi, ya kuma ce: “Mun baiwa jami’an tsaro cikakken ‘yancin yin maganin wannan hauka.
“Na yi Alla-wadai da wadannan hare-haren wuce gona da iri kan kasar nan. Ina mai tabbatar wa jihohi duk wani goyon baya daga gwamnatin tarayya.
“ ina mai yi wa iyalan waɗanda suka mutu ta’aziyya da kuma jaje. Waɗanda kuma suka samu raunuka, Allah Ya tashi kafadun su.”