
A yau Alhamis ne jam’iyyar APC ta tabbatar da gwamnan jihar Filato kuma shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Simon Lalong a matsayin Darakta-Janar na yakin neman zaɓen shugaban kasa.
Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan jim kadan bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Rock Villa, Abuja.
Ya ce, “Mun zo nan ne domin ganin shugaban kasa da yi masa bayani da kuma samun amincewarsa kan tsare-tsaren da muke yi dangane da yakin neman zabe.
“Kuma da zarar mun sami yardarsa, za mu bayyana wa kowa ya ji. Muna tare da Shugaban kasa da kuma ɗaiɗaikun mutanen da za su taka rawa daban-daban a yakin neman zaben.
“ga DG na kamfen a zaune a dama na a nan. Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato.
“Muna masu magana da yawun Festus Keyamo. Mataimakiyar kakakin ita ce Hannatu Musawa. Wannan shi ne abin da muka zo don tattaunawa da shugaban kasa.”
Adamu ya bayyana cewa zaɓen Lalong ya ta’allaka ne kan yadda ya iya yin ayyukan da ake bukata domin tabbatar da nasarar tikitin Tinubu-Shettima a zaɓen shugaban kasa na badi.
“Zai iya aikin sosai. Shugabancin jam’iyyar ya ga cewa zai iya tafiyar da harkokin kamfen din cikin nasara,” in ji shi.