
Gwamna Nasir El-Rufa’i na Nijar Kaduna ya ce idan ya gama mulkin jihar ba zai karɓi wani muƙami daga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba, inda ya ce sai dai ya zama ɗan kwangila.
A wani shiri mai taken ‘Manuniya’ a gidan rediyon VOA Hausa a jiya Juma’a, wanda wakilinmu ya saurara, El-Rufa’i ya ce shi yanzu ya wuce ya karɓi wani muƙami, inda ya ƙara da cewa sai dai a barwa wasu su yi.
A cewar sa, tuni ya faɗa wa Tinubu cewa idan ya ci zaɓe sai dai ya riƙa bashi kwangila, inda ya ƙara da cewa dama ya san Tinubu kuma ya san wasu ministocin da zai naɗa.
Ya ce bai kamata a riƙa nacin riƙe muƙami ba, inda ya nuna cewa kamata ya yi a riƙa bar wa ƴan baya su ma su ɗana.
“Na yi minista ina da shekara 43. Yanzu ina da shekara 63, kawai sai in zo in karɓi muƙamin minista? Ina da ƴaƴa da ƙanne da ƴan uwa, sai in bar musu suma su ɗana.
“Dama na taɓa rubuta littafi kuma na samu kuɗi, saboda haka idan na gama mulki zan sake rubuta wani littafin domin in samu kuɗin fansho da kuma kuɗin makarantar yara.
“Sai kawai na zama ɗan kwangila yadda ake yi, tuni ma na faɗa wa Asiwaju haka. Dama Asiwaju ya san ni kuma na san mataimakin shugaban kasa kuma zan san da yawa daga cikin ministocin da zai naɗa,” in ji El-Rufa’i.