
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wani matashi, Isah Musa, mai shekaru 30 a duniya, bisa zargin sa da yunkurin yin garkuwa da makwabci wanda kuma abokin mahaifinsa ne.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a a Kano.
“A ranar 31 ga Yuli, 2022 da misalin karfe 8:00 wani mazaunin kauyen Makadi da ke karamar hukumar Garko ta jihar Kano ya shigar da kara.
“Mai karar ya ce an kira shi an kuma kuma yi masa barazana ta wayar tarho cewa zai biya Naira miliyan 100, idan ba haka ba za a yi garkuwa da shi ko daya daga cikin ƴaƴansa.
“Ya ce sun yi ciniki kuma daga baya suka daidaita a kan Naira miliyan biyu,” in ji kakakin.
Kiyawa ya ce, mataimakin kwamishinan ƴan sandan jihar, DCP Abubakar Zubairu ne ya umurci tawagar ƴan sanda karkashin jagorancin SP Aliyu Auwal, O/C da ke yaki da masu garkuwa da mutane da su zaƙulo wadanda suka aikata laifin.
Bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma ci gaba da bin diddigi, rundunar ta gano wanda ake zargin, Isah Musa, wanda makwabci ne ga mai karar,” inji shi.
Ya bayyana cewa a binciken farko da ake yi, wanda ake zargin ya bayyana cewa wanda aka yi wa barazanar makwabcinsa ne kuma abokin mahaifinsa ne.
“Ya hada baki da abokinsa da ke zaune a wajen jihar don yin magana a madadinsa,” in ji MlKiyawa.
Kakakin rundunar ƴan sandan ya kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya bayan an kammala bincike