Home Labarai Hajjin 2022: Wani Alhaji daga Jihar Kano ya rasu a Makkah

Hajjin 2022: Wani Alhaji daga Jihar Kano ya rasu a Makkah

0
Hajjin 2022: Wani Alhaji daga Jihar Kano ya rasu a Makkah

 

 

 

 

Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rasuwar ɗaya daga cikin alhazanta na Hajjin bana, Sani Idris Mohammed a garin Makkah.

A wani sako da Babban Sakataren hukumar, Abba Muhammad Dambatta ya aike wa manema labarai, hukumar ta ce marigayin ya fito ne da ga Ƙaramar Hukumar Madobi.

A cewar Dambatta, marigayin ya rasu a ranar Juma’a, sai dai kuma bai faɗi dalilin rasuwar ta sa ba.

Babban Sakataren ya ƙara da cewa tuni a ka yi jana’izar mamacin a Masallacin Harami na Makkah, sannan a ka binne shi a makabartar Shira.