
Babbar kungiyar ‘yan Jamhuriyar Nijar mazauna kasashen waje, HCNE, reshen Najeriya, ta yi kira ga shugabannin kasashen biyu su tattauna kan kisan gillar da ake yi wa ‘yan kasar a kudancin Najeriya.
A cikin wannan mako ne aka kashe wasu ‘yan Nijar bakwai a wasu garuruwa da ke Kudancin Najeriya.
Shugaban kungiyar ‘yan Nijar mazauna Najeriya, Alhaji Abubakar Khalid, ya fada wa BBC cewa biyar daga cikin wadanda aka kashen sun fito ne daga yankin Mada Runfa.
”Muna son gwamnatoci a Najeriya da Nijar su bi mana kadin wadannan mutane namu da aka kashe,” in ji shi.
Ya kara da cewa ya zama dole gwamnatin Nijar ta tashi tsaye ta kare rayuwar ‘yan kasarta a duk inda suke saboda hakkin ne da ya rataya a wuyanta.
”Akalla dan Nijar da aka kashe a Kudancin Najeriya tsakanin jihohin Anambra, da Abia, da Imo, da Enugu daga 2018 zuwa yanzu wallahi ya kai mutum 70 da wani abu, amma idan mun rubuta ma Ambasada ba za a amsa mana ba, ” a cewar Alhaji Abubakar Khalid.
A don haka ya bukaci hukumomi a kasashen biyu da su tashi tsaye su sauke hakkin da ya rataya a wuyansu na kare ‘yan Nijar mazauna Kudancin Najeriya daga hare-hare.
Sai dai akwai masu ra’ayin cewa masu kashe-kashen a Kudancin Najeriyar basu iya bambancewa ba tsakanin yan Arewacin kasar, da kuma yan kasar Nijer da ke zaune yankin.
Ko a karshen mako kungiyar dattawan Arewacin Najeriyar ta yi kira da a kawo karshen kashe ‘yan Arewa da ke zaune Kudancin kasar don kaucewa rikicin da ka iya jefa kasar cikin mummunan yanayi.
Ita ma gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fitar da sanarwar yin tir da kashe ‘yan Arewaci da ke zaune a kudancin kasar, sai dai har yanzu matakan da ta ke dauka basu yi wani tasiri ba.