Home Labarai An hallaka ƙasurgumin kwamandan ƴan fashin daji, Abdulkareem Boss da yaransa 27 a dajin Rugu

An hallaka ƙasurgumin kwamandan ƴan fashin daji, Abdulkareem Boss da yaransa 27 a dajin Rugu

0
An hallaka ƙasurgumin kwamandan ƴan fashin daji, Abdulkareem Boss da yaransa 27 a dajin Rugu

 

 

An kashe ƙasurgumin kwamandan ƴan fashin daji, Abdulkareem Lawal, wanda a ka fi sani da Boss, tare da mayakansa 27 a wani harin jirgin yaki da sojojin Nijeriya su ka kai a Katsina a ranar Asabar da yamma.

PRNigeria ta rswaito cewa sojoji da sauran hukumomin tsaro sun daɗe suna fakon Boss.

Ɗan fashin dajin, wanda ke zaune a dazukan da ke Ƙaramar Hukumar Safana a jihar Katsina , ya addabi mutanen yankin wajen garkuwa da mutane, kisa da kuma satar shanu.

Boss ya yi kaurin suna wajen gayyato sauran ƴan fashin daji su kai hare-hare a jihar Katsina.

Ya na ma cikin ƴan ta’addan da su ka kai hari har yai sanadiyar kashe kwamandan shiyya na ƴan sanda a Dutsin Ma a ranar 5 ga watan Yuli.

Wata majiyar tsaro a sojojin Nijeriya ce ta tabbatar da kisan, inda ya ƙara da cewa an hallaka Boss ne a harin jirgin yaƙi tare da mayakansa su 27.