Home Siyasa Ɗan yayan Buhari, Fatuhu Muhammed ya fice daga APC

Ɗan yayan Buhari, Fatuhu Muhammed ya fice daga APC

0
Ɗan yayan Buhari, Fatuhu Muhammed ya fice daga APC

 

 

 

Ɗan yayan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Fatuhu Muhammed, ɗan majalisar wakilai a jihar Katsina, ya fice jam’iyar APC.

Muhammed shine ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Daura/Sandamu/Mai’adua a majalisar wakilai.

Ya bayyana ficewar tasa daga APC ne a wata wasiƙa, mai kwanan wata 13 ga Yuli.

A wasikar, wacce ya aike wa shugaban jam’iya na mazaɓar Sarkin Yara a Daura, Muhammed ya ce ficewar ta sa ta fara aiki nan take.

Sai dai kuma bai faɗi dalilin da ya sanya ya fice daga jam’iyar ta APC ba.

Amma kuma a watan Mayu, Muhammed ya sha kaye a zaɓen fidda-gwani na jam’iyar APC na majalisar wakilai.