Home Siyasa Ɗan yayan Buhari ya faɗi dalilinsa na barin APC

Ɗan yayan Buhari ya faɗi dalilinsa na barin APC

0
Ɗan yayan Buhari ya faɗi dalilinsa na barin APC

 

 

 

Fatuhu Muhammed, ɗan yayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki ne saboda abokin hamayyarsa ya ci zarafin mahaifinsa.

Daily Trust ta ruwaito yadda Muhammed, ɗin ya fice daga jam’iyyar.

Ɗan majalisar, mai wakiltar mazabar Daura/Mai’Adua/Sandamu ta Jihar Katsina a majalisar dokokin tarayya, ya kasa samun tikitin tsayawa takara bayan ya samu kuri’u 30, yayin da Aminu Jamo, abokin takararsa ya samu kuri’u 117 a zaɓen fidda-gwani.

Tun a zaben-fidda gwanin dai ake ta samun rikici tsakanin sansanonin Fatuhu da Jamo.

Da yake zantawa da wakilin Daily Trust a daren Lahadi, Muhammed ya ce ya bar APC ne saboda abokin hamayyarsa ya ci zarafin mahaifinsa.

“Na samu faifan sauti inda ɗan takararsu (Jamo) ya kira sunan mahaifina, Alhaji Mamman Dan Baffalo tare da cin zarafinsa. Alhaji Mamman Dan Baffallo da Shugaba Buhari uba daya ne da uwa daya.”

“A cikin ’ya’ya 26 da mahaifinsu ya haifa, su ne mazan da suka fito daga uba da uwa daya. Don haka cin zarafin mahaifina shine cin mutuncin shugaban ƙasa.

“Saboda haka na ce tunda batun ya wuce siyasa zuwa zubar da mutuncin iyayena, ba zan iya kara daurewa ba, kuma ba lallai ne in ci gaba da zama a jam’iyyar ba, don haka na yanke shawarar ficewa,” inji shi.