
Shugaban Ƙaramar Hukumar Karu a jihar Nasarawa, James Thomas, ya kafa dokar hana fita a yankin domin duba matsalar tsaro.
Dokar hana fita za ta takaita zirga-zirgar ababen hawa, da rufe dukkan gidajen sinima, Mashaya da gidajen kwana, da duk wasu ayyuka a Ƙaramar Hukumar Karu.
Da yake sanar da dokar ta-bacin a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman (SSA) ga Shugaban Ƙaramar Hukumar kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Danbaba Magaji, kuma ya bai wa ‘yan jarida a Karu, shugaban ya ce dokar hana fita ta zama wajibi ga majalisar ta dauki kwararan matakai don dakile tare da duba matsalar tsaro a yankin,
“Duk da cewa muna samun zaman lafiya a Ƙaramar Hukumar Karu, dole ne a dauki kwararan matakai don dakile yaduwar Matsalar Tsaro daga Babban Birnin Tarayya Abuja, saboda kusancin mu da Abuja”.
A cewar sanarwar, Majalisar ta dauki matakin sanya dokar ta-baci a yankin ne bayan da aka fadada taron zaman lafiya da tsaro da ke duba yanayin tsaro da dukkanin hukumomin tsaro a yankin, inda ta kara da cewa dokar za ta fara aiki daga ranar Alhamis 11 ga watan Agusta, 2022, yana farawa daga 10 na dare zuwa 6 na safe.
“Dole ne mu dauki dukkan matakan tsaro don tabbatar da cewa muna zaune lafiya, saboda masu aikata laifuka suna amfani da yankin mu a matsayin zabin cin gajiyar su. Mun yanke shawarar daukar wannan matakin na riga-kafin da zai fara aiki daga ranar Alhamis 11 ga Agusta, 2022 har zuwa wani lokaci kuma za mu aiwatar da dokar hana fita daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe,” in ji shugaban karamar hukumar.