
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya sha alwashin cewa al’ummar jihar ba za su kaɗa kuri’unsu ga ƴan siyasar da ba su da alaka da jihar.
Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasar a jam’iyyar PDP ya bayyana hakan ne a ranar Litinin din da ta gabata yayin kaddamar da tashar jirgin ruwa ta Orochiri-Worukwo a jihar.
A cewar Wike, al’ummar jihar shirye suke su bijirewa maƙiya jihar ta hanyar kuri’unsu a 2023, yana mai jaddada cewa dole ne su ci gajiyar duk wani Ɗan Takara da zai samu kuri’unsu.
Ya ce, “Idan ka ce Jihar Rivers ba ta da matsala, Jihar Rivers za ta ce maka ba ka da komai a lokacin da ya dace. Idan ba ku son mu, ba za mu so ku ba. Idan kuna son mu, za mu so ku.
“Babu wanda zai yi amfani da kuri’unmu a banza. Kuri’ar mu za ta yi tasiri kuma jihar Rivers ta ci gajiyar duk wanda za mu mara wa baya.
“Siyasa a yanzu ba zabar wani ba ce, abin da za ku yi wa mutanen jihar Ribas ne.”
Wannan ikirari na Wike na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP a matakin ƙasa, musamman ma rigimar da ke tsakanin shi da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugabancin ƙasa a PDP.
Wike da magoya bayansa da magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, sun shiga takun saƙa tun bayan zaɓen Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin Abokin Takarar Atiku.