
Sanannen marubucin nan na Burtaniya, Salman Rushdie na can a wani asibiti da ke Amurka an makala masa na’urar taimakon numfashi, bayan ya samu munanan raunuka sanadiyyar harin da aka kai masa da wuka a birnin New York.
Wakiliyar BBC ta ce wakilin Salman, Andrew Wylie ya ce Salman ya samu rauni a hantarsa, ba zai iya magana ba, kuma akwai yiwuwar zai rasa idonsa daya, yayin da kuma aka yi masa mummunar yanka a wani bangare na hannunsa.
Wani mutum ne dai ya rinka caccaka masa wuka a daidai lokacin da ya hau dandamalai domin yin jawabi kan ƴancin fasaha a wata cibiyar zane-zane.
Salman Rushdie dai ya rinka fuskantar barazana ga rayuwarsa daga wadanda ake wa kallon masu tsattsaurar akidar musulunci tun a shekarar 1989, lokacin da tsohon jagoran Iran, marigayi Ayatollah Khomeini ya bayar da fatawar yin Allah-wadai da littafin da ya rubuta mai taken ‘Satanic Verses’, wato ‘ayoyin sheɗan’, wanda ake wa kallon wani mummunan sabo.
‘Yansanda sun ce sunan wanda ya kai wa Salman wannan hari Hadi Matar, daga jihar New Jersey.