Home Labarai Gwamnatin Tarayya ta baiwa Dantata & Sawoe watanni 4 ya kammala aikin titi a Kano

Gwamnatin Tarayya ta baiwa Dantata & Sawoe watanni 4 ya kammala aikin titi a Kano

0
Gwamnatin Tarayya ta baiwa Dantata & Sawoe watanni 4 ya kammala aikin titi a Kano

 

 

Gwamnatin Tarayya ta baiwa kamfanin Dantata & Sawoe wa’adin watanni huɗu ya kammala aikin titin Western Bypass da ke birnin Kano.

Karamin Ministan Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Umar Ibrahim EL-Yakub ne ya ba da wa’adin a jiya Asabar, lokacin da ya ke duba aikin titin mai tsawon kilomita 26.6.

Ministan ya koka kan yadda aikin ke tafiyar wahainiya.

A cewarsa, ya zama wajibi kamfanin ya kammala aikin nan da karshen shekarar da muke ciki.

“A zahirin gaskiya wannan aikin yana tafiyar wahainiya. Saboda haka, na ba wannan kamfanin nan da karshen watan Disamba ya kammala shi.

“Dole ne a kammala wannan aikin kafin wa’adin gwamnatin Buhari ya kare.

“Za mu samar da dukkan kudaden da ake bukata ga aikin don tabbatar da ba mu bar kowanne aikin da muka fara ba kafin karewar wa’adin gwamnatinmu,” inji shi.

A nasa bangaren Injiniyan da ke kula da aikin, Kasimu Maigwandu, ya ce tashin farashin kayayyaki, musamman man dizal ne babban kalubalensu a aikin.

Sai dai ya ce tuni suka kammala kaso 71.18 cikin 100 na aikin, kuma suna da kwarin gwiwar kammala ragowar kafin wa’adin da aka ba su ya cika.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa titin dai ya faro ne tun daga Na’ibawa a kan hanyar Kano zuwa Zaria kuma ya kare a garin Dawanau da ke hanyar Kano zuwa Katsina.

An bayar da shi ne tun a shekarar 2007 bisa yarjejeniyar kammalawa cikin shekara uku.

Kafin daga bisani gwamnatin Buhari ta sabunta tare da kara wa’adin kwangilar.