Home Labarai Buhari ya sake naɗa Bashir Ahmad tare da ɗaga likkafarsa zuwa babban mataimaki na musamman

Buhari ya sake naɗa Bashir Ahmad tare da ɗaga likkafarsa zuwa babban mataimaki na musamman

0
Buhari ya sake naɗa Bashir Ahmad tare da ɗaga likkafarsa zuwa babban mataimaki na musamman

 

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada tsohon mataimakinsa kan kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin sadarwa na zamani.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya tabbatar da naɗin a wata wasika da aka aike wa Ahmad, mai kwanan wata 20 ga Yuli, 2022.

A cikin wasikar da NAN ta gani a yau Lahadi a Abuja, Mustapha ya ce nadin ya fara aiki ne daga ranar 19 ga Yuli, 2022.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa Ahmad ya yi murabus daga mukaminsa na tsohon mataimakin shugaban kasa bisa ga umarnin shugaban kasa na cewa duk masu rike da mukaman siyasa da ke son tsayawa takara da su yi murabus.

Sai dai kuma ya sha kaye a yunkurin sa na samun tikitin takarar, a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na mazabar Gaya/Ajingi/Albasu.

Ahmad ya fusata kan yadda aka gudanar da zaben fidda-gwanin, yana mai cewa an tafka magudi.