Home Siyasa Shekarau ya magantu kan rahoton ficewarsa da ga NNPP zuwa PDP

Shekarau ya magantu kan rahoton ficewarsa da ga NNPP zuwa PDP

0
Shekarau ya magantu kan rahoton ficewarsa da ga NNPP zuwa PDP

 

 

Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ya yi kira ga magoya bayansa da su yi watsi da duk wani labari da ake yaɗa wa cewa zai fice daga jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar PDP.

Mai magana da yawun Sanata Shekarau, Dakta Sule Ya’u Sule, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Talata a Kano.

Sule Ya’u Sule ya ce al’umma su yi watsi da duk wani labari da ake yaɗa wa, inda ya ce a cikin makon nan tsohon gwamnan zai fidda matsayarsa a siyasa.

” A halin yanzu dai jama’a su yi watsi da duk wani labari a kan siyasar Malam Ibrahim Shekarau. A cikin makon nan da muke ciki za mu ba da cikakken bayani game da Siyasar Gidan Sanata Malam Ibrahim Shekara,” inji Dr. Sule Ya’u Sule

A safiyar yau Talata ne dai Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tuni Shekarau ya kammala shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar PDP sakamakon tayin da Atiku Abubakar ya yi masa da kuma gwaɓaɓan alƙawura.