
Cif Duro Onabule, tsohon dan jarida kuma tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badsmasi Babangida ya rasu.
Onabule, a cewar wani makusancinsa, Eric Teniola, ya rasu a jiya Talata yana da shekaru 83 a duniya.
“Cif Duro Onabule ya mutu da yammacin yau,” wata majiya ta iyali ta shaida wa jaridar The Guardian.
Kawo yanzu dai ba a san musabbabin mutuwarsa ba.
An haifi Onabule a garin Ijebu-Ode, jihar Ogun, a ranar 27 ga Satumba, 1939.
Ya halarci Makarantar Grammar CMS da Makarantar Aikin Jarida, London.