
Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta shawarci ƴan Najeriya da su rungumi al’adar sanya na’urorin kyamarar tsaro, da a ka fi sani da CCTV a wuraren kasuwancinsu da kuma gidajensu domin daƙile taɓarɓarewar tsaro a ƙasar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi, SP Chris Anyanwu ya fitar a yau Juma’a a Abakaliki.
Anyanwu ya bayyana cewa na’urar tana da amfani wajen samar da tsaro.
Ya ƙara da cewa na’urar ta na taimaka wa ayyukan ƴan sanda ta ɓangarori da dama, musamman wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.