Home Siyasa 2023: Ni kaɗai ne na fito takarar gwamna ba ta alfarma ba — Bashir I. Bashir

2023: Ni kaɗai ne na fito takarar gwamna ba ta alfarma ba — Bashir I. Bashir

0
2023: Ni kaɗai ne na fito takarar gwamna ba ta alfarma ba — Bashir I. Bashir

 

 

Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyar Labour Party, LP, Injiniya Bashir Ishaq Bashir, ya ce shi kaɗai ne wanda ya samu tikitin takarar gwamna a jihar ba ya hanyar alfarma ba.

Injiniya Bashir ya bayyana haka ne a wata hira ta kai tsaye da wasu zaɓaɓɓun gidajen rediyo a Kano a yau Asabar da daddare.

A cewar sa, sauran jam’iyun, ƴan takararsu sun samu tikitin ne sakamakon wani iko na masu gidansu a siyasa, ba wai zaɓin al’umma ba.

Ya ƙara da cewa shi kaɗai ne ya shiga jam’iya, ya kuma samu takara ta hanyar bin ra’ayin al’umma da ƙa’idojin dimokuraɗiyya, ba wai ta “ƙarfa-ƙarfa” ba.

“Duk sauran jam’iyyun, yan takara ne da su, waɗanda na wani mutum ne ƙwaya ɗaya, ya ɗora su a takarar.

“Mu kadai ne mu ka shiga jami’ya, mu ka tsaya da kafar mu, ba alfarmar wani muka nema ba, ba wani ne ya ɗora mu ba, ba kuma ƙarfa-ƙarfa a ka yi a ka ɗora mu ba,” in ji shi.

Injiniya Bashir, wanda ya fara tsaya wa takara a jam’iyar APC, ya ce kyawawan ƙudirori da hangen nesa ne ya sa su ka shiga jam’iyar LP kuma ta basu dama domin kawo canji ma gari.

Ya kuma yi alkawarin samar da wutar lantarki mai kimanin wat 50 a watanni shida na farkon mulkinsa, inda ya ƙara da cewa jam’iyar LP, idan ta samu dama, za ta kawo canjin da ake buƙata a ƙasa da jihar Kano.