
Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya, IRT, sun kama wasu daliban jami’ar Ambrose Alli da ke Ekpoma su 11 bisa zarginsu da hada baki da kungiyoyin asiri da kuma mallakar haramtattun makamai ba bisa ka’ida ba.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai a yau Alhamis a Abuja.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a watan Yuli a wurare daban-daban a Epkoma bayan samun bayanan sirri kan ayyukan kungiyoyin asiri a yankin.
Kakakin ƴan sandan ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifinsu na cewa su ƴan kungiyar asiri ne, Black Ax Confraternity, a lokacin da ‘yan sanda ke gudanar da bincike.
Ya ce an kwato bindigu kirar AK47 guda biyu, kananan bindigu guda uku, bindiga ƙirar gida guda daya, gidan jera harsashi AK47 guda biyu da harsashi na AK47 guda 22 daga hannun wadanda ake zargin.
A cewarsa, sauran kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da harsashi K2 guda 17 da kuma harsashi guda uku.