Home Labarai Ba mu kama wani mai safarar makamai ta jirgin sama a Neja ba — Ƴan Sanda

Ba mu kama wani mai safarar makamai ta jirgin sama a Neja ba — Ƴan Sanda

0
Ba mu kama wani mai safarar makamai ta jirgin sama a Neja ba — Ƴan Sanda

 

Rundunar ƴan sanda a jihar Neja ta ce ba ta kama wani ɗan ƙasar waje ya na raba wa ƴan ta’adda makamai ta jirgin sama mai saukar ungulu ba.

Kwamishinan ƴan sanda na jihar, Monday Kurya, ya ce sam-sam hakan bai faru ba a ko ina a faɗin jihar.

Kurya ya siffanta rahoton a matsayin labarin ƙarya da ake ta yaɗa wa a kafafen sadarwa.

Kurya ya yi kira ga mazauna jihar da su zama masu bin doka da kuma riƙa sanya ido da bada bayanan mutanen da ba a amince da su ba.

Ya kuma tabbatar da cewa za a rufa asirin duk wanda ya kawo bayani.