
Gwamnatin tarayya ta bada umarnin nemo dan kwangilar da yayi aikin gina gadar Ado Bayero, da ke Gyadi Gyadi wadda akafi sani da Gadar Lado a jihar Kano.
Kimanin wata guda kenan da lalacewar wani sashi na gadar, wanda hakan ya yi sanadiyyar rufe hannun da ke yin hanyar Na’ibawa.
Karamin Ministan Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Umar Ibrahim El-yakub ne ya bayyana hakan yayin da ya ke duba yadda aikin titin Kano zuwa Zaria ke gudana a jiya Asabar.
“Wannan gadar tana da matukar muhimmanci ga al’ummar jihar kano dama baƙi da su ke shigo wa jihar, don haka ya zama wajibi ɗan kwangilar da ya yi aikin ya dawo domin gyara ta don al’umma su cigaba da amfana da ita,” Inji El-Yakub
Minista yace tuni ya bada umarnin a nemo ɗan kwangilar da ya yi aikin gadar saman, wacce ta ke daura da Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano domin ya fara gyaranta.
” Cikin wannan makon da za mu shiga, za ku ga anzo an gyara gadar saboda muhimmancin ta ga al’ummar jihar Kano da kuma harkokin sufuri da tattalin jihar Kano da na ma ƙasa baki ɗaya,”