
Ɗan takarar shugabancin kasa a inuwar sabuwar jam’iyya ta hamayya, NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce jam’iyyarsa za ta kwace mulki daga hannun gwamna Babagana Umara Zulum a zaɓen 2023.
Kwankwaso ya shaida hakan ne a birnin Maiduguri lokacin bude ofishinsu na kamfen a jiya Asabar.
Sanata Kwankwaso ya ce jam’iyyarsa ce za ta lashe zaɓe a Najeriya tun daga matakin jihohi har Tarayya.
Sannan ya buƙaci magoya bayansa su kasa su kuma tsare kamar yada ya aiwatar a Kano a lokutan zaɓe.
Kwankwaso ya je Maiduguri ne kwana biyu bayan hukumar raya birane ta jihar ta rufe ofishinsu kafin daga bisani gwamna Zulum ya umarci a sake buɗe ofishin.