Home Labarai Ƴan Sanda sun kama masu garkuwa da mutane 2 a Jigawa

Ƴan Sanda sun kama masu garkuwa da mutane 2 a Jigawa

0
Ƴan Sanda sun kama masu garkuwa da mutane 2 a Jigawa

 

Rundunar yan sandan jahar Jigawa ta tabbatar da samun nasarar kama wasu mutane biyu (2) da ake zargin su da yin garkuwa da mutane a faɗin jahar .

Mai magana da yawun rundunar Ƴan Sandan Jahar DSP Shiisu Lawan Adamu ne yabayyana hakan a cikin wata sanarwa da rabawa manema labarai a ranar Asabar.

DSP Shiisu Adamu ya ce ” a ranar 24 ga watan Agusta 2022 suka samu rahotan cewa anga wani mutum mai suna Muhammad Sama’ila mai shekaru 45 mazaunin Garin Madari a ƙaramar hukumar Warawa ta jahar Kano, an Sassare shi a sassan jikinsa .

Bayan samun rahotanne suka garzaya da mutumin zuwa asibiti domin duba lafiyar sa ,bayan ya samu sauƙi ne mutumin ya bayyana mu su cewa ” tun a ranar talata 22 ga watan Agusta 2022 aka yi garkuwa da shi daga jahar Kano inda aka shi ƙauyen Nisan Marke wajen wasu Makiyaya a jahar Jigawa.

Mutumin ya ƙara da cewa a ƙoƙarin da yake yi ne na gaduwa ne daga hannun masu Garkuwa da Mutanen ɗaya daga cikin su yaji masa raunuka.

DSP Shiisu Lawan Adamu ya ƙara da cewa tuni Kwamishinan yan sandan jahar, CP Aliyu Saleh Tafida ya tashi tawaga ta musamman, ƙarƙashin jagorancin Baturan ƴan sanda na Ringim, SP Shehu Hamdullahi ,da haɗin gwiwar jami’an vigilante, waɗanda suka kai sumamen a maɓoyar su dake Nisan Marke.

Da isar jami’an kuwa su ka samu nasarar nasarar cafke Abdurrazaq Musa mai shekaru 40, mazaunin Garin Gargunna a Ƙaramar Hukumar Ɓabura, da kuma wani mai suna Hassan Jimau, mai shekaru 30 dake garin Nisan Marke.

Dukkan waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu da cewar sune suka yi garkuwa da mutumin , su da wasu ƙasurguman masu garkuwa da mutane su 8 da rundunar ta baza neman su ruwa a jallo.

Tuni dai waɗanda ake zargin aka miƙa su sashin gudanar da binciken Laifuka na masu garkuwa da mutane dake jahar Kano (anti kidnapping Kano) domin faɗaɗa bincike akan su.