Home Ilimi Yajin aiki: Jami’o’i mallakin jihohi sun fara yi wa ASUU tutsu

Yajin aiki: Jami’o’i mallakin jihohi sun fara yi wa ASUU tutsu

0
Yajin aiki: Jami’o’i mallakin jihohi sun fara yi wa ASUU tutsu

 

Jami’o’i mallakar gwamnatocin jihohin Najeriya na ci gaba da komawa bakin aiki, duk da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ASUU ke yi a duk fadin kasar.

Al’amarin da ke nuni da yadda goyon bayan da yajin ke samu yake ta kara zaizayewa, yayin da kungiyar malaman ta yi tsayuwar daka kan matsayinta, cewa sai gwamnatin tarayya ta inganta manyan makarantun nata a sassan kasar.

BBC ta rswaito cewa sai dai yayin da wasu ke kira ga bangarorin ASUU da na gwamnati da ke tattaunawa su rika taunawa suna hurawa don samar da mafita, wasu kuwa suna ganin daliban da yajin aikin ya shafa da iyayensu ne ba su dauki lamarin da muhimmanci ba.

Rahotanni dai sun ce, Jami’ar Jihar Ekiti, ita ce jami’a ta baya-bayan nan da ta juya wa yajin aikin na kungiyar ASUU baya, bayan shigen wannan mataki da jami’o’in Jihohin Legas da Osun da Kwara da Kaduna suka dauka.

Kodayake kungiyar ta bayyana tababar kasancewar wasunsu a cikin mambobinta.

Farfesa Abdullahi Ashafa, Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna na riko, ya bayyana dalilan bude tasu jami’ar, inda ya ce:

“Abin ya tsawaita, babu dalili kuma cutuwa muke yi, ɗalibanmu suna zaune a gida, iyaye sun gaji da ganin ƴayansu a gida, mu ma mun gaji da zama a gida,” in ji Farfesa Abdullahi.

Ya bayyana cewa gwamnati ta ce tana kokarin biyan albashi amma ba a aiki, wanda wannan ne ya sa suka buɗe jami’a domin a koma karatu duk da a cewarsa har yanzu akwai wasu malamai ƙalilan da ba su dawo ba. Da yawa dai ana ta yamadidi ne, cewa kungiyar ta ASUU ta yi tsayuwar gwamen jaki kan yajin aikin nata ne tsanta, bisa batun albashi. Al’amarin da Abubakar Danlami Alhassan, malami a tsangayar koyar da aikin jarida ta Jami’ar Bayero ta Kano, ya ce ba haka abin yake ba:

“Magana ce ta kayan aiki da inganta su kansu jami’o’in, a gyara makwancin ɗalibai, a gyara azuzuwa, a kawo isassun takardu a kawo isassun kayan bincike da sauran su,” in ji Malam Abubakar.

A halin yanzu dai harkokin ilimi suna nan cikin halin kaka-nika-yi a jami’o’in tarayya da ‘yan rakiyarsu na jihohi, tun fiye da watanni 6 da suka gabata.

Kuma bisa la’akari da yadda abin ke tafiyar dodon katantanwa, ana hangen shawo kan wannan matsala ya zama tamkar neman karon kalgo.