Home Labarai Arsenal za ta yi wa Henry jarrabawar gwajin daukar aiki a matsayin mai horaswa

Arsenal za ta yi wa Henry jarrabawar gwajin daukar aiki a matsayin mai horaswa

0
Arsenal za ta yi wa Henry jarrabawar gwajin daukar aiki a matsayin mai horaswa

Daga Hassan Y.A. Malik

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal za ta gana da tsohon dan wasan gabanta, Thiery Henry a kokarin da kungiyar ke yi na nemawa Arsene wenger mai murabus madadi.

Kodayake dai Mikel Arteta shi ne wanda hukumomi a kungiyar suka fi goyon baya ya gaji Arsene Wenger din, amma har yanzu kungiyar na ganawa da wasu masu horaswan da ke da sha’awar rike kungiyar.

A baya ma dai sai da Arsenal ta tattauna da Patrick Vieira kan batun neman wanda ya cancanci ya gaji Wenger, haka kuma kungiyar ta Arsenal ta shirya tattaunawa da Henry don shi ma a bashi dama duk kuwa da cewa bai taba rike wata kungiya ba.

Zuwa yanzu dai Henry shi ne mataimakin kocin tawagar kwallon kafa ta Belgium haka kuma yana yi wa gidan talabijin na Sky Sports fidar wasanni gabanin a buga da bayan an tashi wasannin.