
Shahararren malamin addinin Muslunci, Sheikh Tijjani Bala Kalarawai ya ka hankalin mawaƙan begen Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da su riƙa kiyaye kalamai a waƙoƙinsu.
Malamin ya yi gargaɗin me jiya Laraba a Kano, inda ya ce mawaƙa da dama, musamman masu begen Manzon Allah, su na fadar kalaman da ba su dace ba.
A cewar Sheikh Kalarawai, mawakan bege na furta kalamai da ba su dace ba a waƙoƙinsu, inda ya ce hakan na iya kai mutum ga halaka.
Ya yi kira ga mawaƙan da su riƙa tuntuɓar malamai idan za su yi waka domin su saka su a hanya.
“Ina jan hankalin masu wakoki, musamman na begen Manzon Allah, da su kiyaye, su riƙa tuntubar malamai domin su saka su a hanya.
“A gaskiya a na furta wasu kalamai ga Manzon Allah da basu dace ba a cikin wakoki. Ya kamata a samu ilimi sosai kafin a fara bege,” in ji Sheikh Kalarawai