Home Labarai Banufen da ya mutu a 1975 ya dawo ya kuma mutuwa

Banufen da ya mutu a 1975 ya dawo ya kuma mutuwa

0
Banufen da ya mutu a 1975 ya dawo ya kuma mutuwa

Banufen da ya mutu a shekarar 1975 kuma ya dawo bayan da aka kusa yin jana’izarsa ya kuma mutuwa a ranar Larabar da ta gabata.

Dan uwan mamacin Gana Solomon ne ya tabbatar da haka ga manema labarai ta wayar tarho a daren jiya Alhamis.

Mamacin da aka bayyana sunansa da Alhaji Gana, ya rayuwa shekaru 43 bayan da yayi mutuwar farko, inda aka rusa kukan mutuwarsa, har aka shirya bizne shi amma ya dawo.

Mutumin dai an yi takadda sosai a lokacin mutuwarsa da kuma dawowarsa a shekarar 1975, inda har sai da ta kai Etsu Nupe da kansa a lokacin ya shiga cikin lamarin tare da jimamin al’amarin.

Sai dai yanzu dai mutumin yayi mutuwar gaba daya, domin kuwa tuni aka bizne shi a kushewarsa.