Home Ilimi Kawu Sumaila ya baiwa daliba gurbin karatu kyauta a jami’arsa ta Al-Istiqama

Kawu Sumaila ya baiwa daliba gurbin karatu kyauta a jami’arsa ta Al-Istiqama

0
Kawu Sumaila ya baiwa daliba gurbin karatu kyauta a jami’arsa ta Al-Istiqama

 

A kokarinsa na bunƙasa rayuwar al’umma ta fannin ilimi, Mamallaki kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na Jami’ar Al-istiqama, Sumaila (AUSU), Abdurrahman Sulaiman Kawu Sumaila ya baiwa wata yarinya, Rumasa’u Muhammad Adam gurabin karatu kyauta a jami’ar biyo bayan kwazon da ta yi a jarrabawar WAEC ta 2022.

Rumasa’u wacce take yar asalin garin Kachako ce da ke Ƙaramar Hukumar Takai a jihar Kano, ta samu kyakyawan sakamako a jarabawar, Inda ta cinye dukka darussa 9, gami da lissafi da ingilishi a jarrabawar watan Mayu/Yuni ta WAEC .

A cewar sanarwar da kawu Sumailan ya sa wa hannu da kansa, wannan karimcin ya yi daidai da kokarinsa na alfahari da ilimi a cikin al’umma ta hanyar yi wa al’umma hidima tare da cimma manyan manufofin bunkasa kyawawan dabi’u da ilimi ga dalibai a cikin jama’ar da ke kusa da wajen da kuma sauran su.

An ba ta izinin yin karatun digiri na shekaru huɗu a tsangayar koyar da ilimin kimiyyar lafiya a Jami’ar ta AL-Istiqama, Sumaila, farawa daga shekarar karatu ta 2022/2023 .

A lokacin da yake mika godiyarsa ga Kawu Sumaila bisa karamcin da ya yiwa yar, Hamza Safiyanu Kachako, a madadin al’ummar Takai/Kachako, ya mika godiyarsa ga Allah madaukakin sarki, ya kuma yabawa Kawu Sumaila bisa wannan karimcin.

Daga nan sai ya bukaci wadda ta ci gajiyar da ta dauki wannan lambar yabo a matsayin kyauta ta musamman sannan ta mayar da hankali ta saka abun da akai mata ta hanyar ninka kokarinta a lokacin da take karatu a jami’ar Al-Istiqama da ke Sumaila.

Sannan ya umarce ta da ta zama jakadiya ta gari wadda sauran mutane da iyayenta za su yi alfahari da ita.

“Allah ya sa wannan kokari ya zama alheri ga daukacin al’ummar musulmin duniya,” in ji shi.