Home Labarai Ƴan Sanda sun kama magidancin da ya kashe mahaifansa da taɓarya a Jigawa

Ƴan Sanda sun kama magidancin da ya kashe mahaifansa da taɓarya a Jigawa

0
Ƴan Sanda sun kama magidancin da ya kashe mahaifansa da taɓarya a Jigawa

 

 

 

Rundynar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wani magidanci, mai suna Munkaila Ahmadu, wanda ya kashe mahaifinsa mai shekaru 70 kuma dagacin kauyen Zarada Sabuwa, a Karamar Hukumar Gagarawa a Jihar Jigawa.

Hakazalika, ya kashe mahaifiyarsa mai shekaru 60, duk da taɓarya, inda ita ma nan take ta mutu.

Munkaila, mai shekaru 37 ya jefa mutanen ƙauyen Zaranda Sabuwa cikin jimami a dalilin wannan mummunar aika-aika da yanyi.

Jaridar Premium Times Hausa ta rawaito cewa bayan haka Munkaila bai tsaya a nan ba sai da ya ji wa wasu mutane biyu rauni a ƙauyen.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, wanda shine ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce tuni ƴan sanda sun damƙe Munkaila kuma ya na tsare a hannun su.

” An tabbatar cewa Munkaila ya bubbuga wa mahaifi da mahaifiyarsa taɓarya bayan dukan tsiya da ya yi musu. Ko da aka kai su asibiti an tabbatar sun rasu tun a gida.

A karshe dai Kwamishinan ƴan sandan jihar ya umarci da a miƙa wannan lamarin gabadayansa ga fannin binciken manyan laifuka na rundunar.

Sai dai kuma ba a kai ga gano cewa ko Munkaila na da taɓin hankali ko akasin haka ba, duba da irin ɗanyen aikin da ya aikata.