
An kama wani mawakin zamani na Nijeriya, Ice Prince Zamani bisa zargin guduwa da ɗan sanda.
Kakakin rundunar ƴan sandan na jihar Legas, Ben Hundeyin ya tabbatar da hakan a yauJuma’a.
Hundeyin ya bayyana lamarin da ya kai ga kama Ice Prince a shafin sa na Twitter.
Ya ce “Da karfe 3 na safiyar yau, an tayar da @Iceprincezamani saboda tukin mota ba tare da lasisi ba.
“Sai ya amince a kai shi Caji-ofis. Daga nan ne kuma ya yi awon gaba da ɗan sandan da ke cikin motarsa, inda ya kai masa hari tare da yi masa barazanar jefa shi a cikin kogi.
“An kama shi kuma za a gurfanar da shi a yau,” Hundeyin ya rubuta.
Ice Prince ya yi suna bayan ya fito da waƙar “Oleku”, ɗaya daga cikin wakokin da aka fi yin mai-mai ɗin su a tarihi a Najeriya. Ya kuma ci kyautar girma ta 2009 Hennessy Artistry Club Tour.