
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta mayar da almajirai 805 gaban iyayensu Kananan Hukumomi 44 na jihar.
Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Dakta Haruna Ibn-Sina ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a jiya Juma’a a hedikwatar Hisbah da ke Sharada a Kano.
Ya ce mabaratan 805 da suka kunshi mata 536 da maza 279 ‘yan asalin jihar Kano ne.
Ya ce suna daga cikin mutane 931 da ake zargin mabarata ne da jami’an hukumar Hisbah suka kora bisa zarginsu da karya dokar hana barace-barace a cikin birnin Kano.
Malam Ibn-Sina ya ce, wadanda suka fito daga jihohin da ke makwabtaka da su, an taimaka wa gwamnatocin jihohinsu daban-daban wajen mik6a su ga ƴan uwansu, yayin da wasu ke samun kulawa daga hukumar.
A cewarsa, daga cikin 931 da aka kwashe, 320 maza ne yayin da 611 mata ne.
Malam Ibn-Sina ya yi zargin cewa wasu daga cikin mabaratan na daga cikin wadanda ake zargi da satar wayoyi da hada kai da masu laifi a riƙa addabar mutane.
Ya bukaci iyaye da su kara kaimi ga kokarin gwamnati ta hanyar baiwa ‘ya’yansu tarbiyyar da ta dace.