Home Siyasa Kotu ta kori ƙarar da aka shigar a kan Natasha Akpoti

Kotu ta kori ƙarar da aka shigar a kan Natasha Akpoti

0
Kotu ta kori ƙarar da aka shigar a kan Natasha Akpoti

 

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Lokoja a jiya Juma’a ta kori ƙarar da ke kalubalantar Natasha Akpoti-Uduaghan ta jam’iyyar PDP.

A ranar 25 ga watan Mayu ne Natasha ta lashe zaɓen fidda-gwani gwani na jam’iyyar da INEC ta sanya wa ido, a matsayin ƴar takarar Sanata ta jam’iyyar PDP na mazaɓar Kogi ta Tsakiya a babban zaɓen 2023.

Sai dai abokin takararta, Adamu Atta ya ƙalubalanci zaɓen a gaban babbar kotun tarayya.

Sai dai alkalin kotun, Mai shari’a Peter Malong, a cikin hukuncin da ya yanke, ya yi watsi da ƙarar a kan cewa ba ta cika sahihiya ba kuma ba ta da ƙwari.

“Duba da yadda wannan karar ta fito, da farko an shigar da ita ba bisa ka’ida ba kamar yadda lauyan wanda ake ƙara ya lura, don haka wannan kotun mai girma ba ta da hurumin sauraren karar.

Don haka, karar ba ta cika ka’ida ba kuma saboda haka na yi watsi da ita gaba daya,” in ji alkalin.