Home Siyasa Jam’iyyar ADC ta dakatar da ɗan takararta na shugaban ƙasa

Jam’iyyar ADC ta dakatar da ɗan takararta na shugaban ƙasa

0
Jam’iyyar ADC ta dakatar da ɗan takararta na shugaban ƙasa

 

Jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC) a Najeriya ta dakatar da ɗan takararta na shugaban ƙasa Dumebi Kachikwu, tana zargin sa da yaɗa bidiyon “cin zarafi” da sauran laifuka.

Kazalika, jam’iyyar ta bayyana kalaman da ta ce Mista Kachikwu ya yi a bidiyon a matsayin “rashin dattako da ɓata suna da nuna ɗabi’ar da ba ta dace da wanda ke son ya zama shugaban ƙasa ba”.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Asabar mai sa hannun Mataimakin Shugaban ADC Bamidele Ajadi, jam’iyyar ta ce ta ɗauki matakin ne bayan taron Kwamatin Gudanarwa ranar Juma’a.

“Kwamatin Gudanarwa ya damu matuƙa kan bidiyon ɓata suna da Dumebi Kachikwu ya wallafa kuma ya yaɗa da zimmar ƙasƙantar da jam’iyyar ADC mai neman sauyi da shugabanninta,” a cewar sanarwar.

Sai dai Mista Kachikwu bai mayar da martani ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

A watan Fabarairu mai zuwa ne za a gudanar da babban zaɓe a Najeriya, inda ‘yan ƙasar za su zaɓi shugaban ƙasa da gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya da na jihohi.