
Sanatan Kano ta Tsakiya, Ibrahim Shekarau ya sha alwashin cewa shi zai kawo wa ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar PDP, Atiku Abubakar ƙuri’u mafi rinjaye a jihar Kano sama da na Rabi’u Kwankwaso na NNPP da Bola Tinubu na APC a zaɓen 2023.
Shekarau ya bayyana hakan ne a wata hira da a ka yi da shi a gidan talabijin na AIT a jiya Talata.
Tsohon gwamnan Kano ɗin ya ce yana da ɗumbin masoya ƴan dangwale, waɗanda su ne su ka zaɓe shi a zaɓen 2003, lokacin da ya kayar da Kwankwaso, da kuma 2007.
Hakan ne Shekarau ya bayyana yaƙinin cewa masoyan na sa suna nan kuma su zasu zaɓi Atiku Abubakar a 2023.
” A shekarar 2003 na kayar da Kwankwaso da Ganduje a takarar kujerar gwamna a Kano lokacin a Jam’iyyar ANPP, na basu ratar sama da kuri’a dubu dari shida (600,000 ).
“Sannan a zaɓen 2007 sun sake tsayawa takarar gwamna na kayar dasu, don haka a zaɓen 2023 zan kawo wa Atiku kuri’ar jihar Kano Insha Allah”. Inji Shekarau
Shekarau wanda kwanan nan ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP, ya kuma ƙara da cewa zai haɗo kan mutanen sa na jihohi daban-daban da ke ƙasar nan, waɗanda su ka zaɓe shi lokacin da ya yi takarar shugaban ƙasa domin su zaɓi Atiku Abubakar ko a wacce jam’iyya suke a zabe mai zuwa.