Home Siyasa 2023: Ƴan siyasa za su iya cin zaɓe ba tare da tonon silili ba — Fashola

2023: Ƴan siyasa za su iya cin zaɓe ba tare da tonon silili ba — Fashola

0
2023: Ƴan siyasa za su iya cin zaɓe ba tare da tonon silili ba — Fashola

 

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, SAN, ya ce ƴan siyasar Najeriya za su iya lashe zaɓe a 2023 ba tare da kambama matsalolin Nijeriya, ko yi mata tonon silili a idon duniya ba.

Fashola ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis a Legas, yayin da ya ke gabatar da babban jawabi a Lakca na shekara-shekara, mai taken: “Zaben 2023 da makomar Dimokuradiyyar Nijeriya.”

“Za mu iya cin zabe ba tare da mun kambama matsalolinmu ba. Za mu iya yin hakan ta hanyar yin aiki mai inganci da kuma samar da mafita sahihiya.

“Za mu iya cin zaɓe ba tare da mun yi wa ƙasarmu tonon silili a gaban al’ummar duniya ba. Za mu iya yin haka ta hanyar tabbatar da abubuwa masu yiwuwa a Najeriya ba ta hanyar kambama matsalolin ƙasar ba.

Ya ce duk da cewa dimokuradiyya ta bada ƴancin faɗin albarkacin baki, amma da yawa sun tsunduma cikin yin yarfe, cin zarafi ta yanar gizo, kiyayya, da zage-zage na baki a wasu lokuta ko magana kan kabilanci ko addini.