
Kwamitin Gudanarwa, NWC, na jam’iyyar NNPP mai kayan marmari, rusa shugabannin zartaswar jam’iyyar a Jihar Osun sabo da rikicin shugabanci.
Rushewar na kunshe ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 11 ga watan Satumba, 2022 mai dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar na kasa, Dipo Olayoku.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, ya samu kwafin wasikar a yau Talata a Osogbo.
An rusa shugabannin zartaswas ne biyo bayan kaɗa kuri’ar rashin goyon;baya da shugaban majalisar, Dokta Tosin Odeyemi, da mambobinta suka yi.
Kwamitin na NWC ya kuma naɗa kwamitin riko mai mutum shida a madadin rusassun shugabannin zartarwas.
Kwamitin zai shafe watanni uku yana jan ragamar jagorancin jam’iyyar, a ƙarƙashin jagorancin Abdulsalam Abdulateef.