
Ɗan Takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya yi alkawarin yaƙar yunwa idan yan Nijeriya su ka zaɓe shi.
Wannan na ƙunshe a cikin sanarwar da ya fitar mai dauke da sa hannun Abdulrasheed Shehu, hadimin Atiku kan bangaren kafafen yaɗa Labarai.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wannan alkawarin ne yayin taron tattalin arziki da bangarori masu zaman kan su suka shirya a Legas a yau Talata.
A jawabin da ya gabatar, mai taken ”Nijeriya na Ado da kayan Aro” ɗan takarar na PDP, ya yi amfani da damar wajen yaba wa shugaban cibiyar kasuwanci da kuma mambobin ta saboda kirkiro wannan taro na kwararru inda aka tattauna muhimman abubuwan da ke addabar ci gaban Najeriya.
Ya bayyana yadda ya samu nutsuwa da kwancewa a tsakanin gaggan Yan kasuwar Maza da mata, Wanda lasancewa sa mutumin da ya fito Daga bangare Mai zaman kansa, sai ya je shi tamkar a cikin gida, inda ya bayyana taron a matsayin na masu tunani iri Daya.
Yace a lokuta na rashin tabbas, abu ne mai kyau ga shugabannin Yan kasuwa da na siyasa su rika taka-tsantsan kafin daukar matakai.
Yace matakan da muka dauka yau, zasu bayyana kan harkokin mu na gobe.