Home Labarai A shirye mu ke da mu janye yajin aiki — ASUU

A shirye mu ke da mu janye yajin aiki — ASUU

0
A shirye mu ke da mu janye yajin aiki — ASUU

 

 

Shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana cewa ƙungiyar a shirye take ta kawo karshen yajin aikin da ta kwashe watanni bakwai ta na yi.

Osodeke, ya ce za a iya cimma hakan ne kawai idan ƙungiyar ta cimma yarjejeniya ta gaskiya da gaskiya da gwamnatin tarayya.

Osodeke ya ba da wannan tabbacin ne a Abuja a yau Alhamis, a wani taro na ƙasa da ƙasa kan ilimin manyan makarantu.

“A kan dukkan wadannan batutuwa, mun bai wa gwamnati mafi karancin abin da za mu iya karɓa, amma ba su mayar da martani kan batun sake farfaɗo da Jami’o’i ba, da batun alawus-alawus da ake samu da kuma batutuwan da muka tattauna.

“Mun yi shawarwari kuma mun amince da su sanya hannu kuma wannan abu ne mai sauki, a kwana ɗaya ma za a iya cimma matsaya.

“Akan tsarin albashi na UTAS da IPPIS, mun ce ku fitar da rahoton gwajin da kuka yi, mu duba wanda ya zo na farko mu ɗauka kamar yadda muka amince.

“Don haka mun ba su mafi karancin abin da muke so kuma dole ne muma mu sassauta kuma za su iya yin hakan a rana ɗaya idan ana so,” inji shi.