
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, Limited, da wasu rassansa da su dage sukammala gyaran sashe na 4 na hanyar Gabas zuwa Yamma.
Ɓangaren titin na daga zagayen Eleme zuwa mahaɗar Onne, ta hanyar shirin tsarin biyan haraji.
Buhari ya bayyana hakan ne a wajen bikin buɗe taron majalisar yankin Neja Delta karo na 5 a garin Uyo, a jiya Alhamis.
Aikin titin Gabas zuwa Yamma, wanda ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya ke gudanarwa a halin yanzu, shi ne aikin samar da ababen more rayuwa mafi girma a Nijeriya.
“Hanyar hanya ce mai matukar muhimmanci, wacce ta hada manyan biranen kasar nan da suka yi five hada-hadar kasuwanci da cinikayya a yankin.
“Za a magance wannan cikin gaggawa, la’akari da mahimmancin hanyar ga tattalin arzikin kasa,” in ji Buhari.
Buhari, wanda ya samu wakilcin Mohammed Abdullahi, Ministan Muhalli, ya tabbatar da cewa kammala aikin titin Gabas zuwa Yamma shi ne babban fifiko ga wannan gwamnati.