Home Siyasa Dandazon al’umma sun tarbi Kwankwaso a Jihar Delta

Dandazon al’umma sun tarbi Kwankwaso a Jihar Delta

0
Dandazon al’umma sun tarbi Kwankwaso a Jihar Delta

 

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya ziyarci birnin Warri na jihar Delta domin buɗe ofishin yaƙin neman zaben dan takarar Sanatan Delta ta Kudu a zaɓen 2023.

Kwankwaso wanda ya isa garin Warri a jiya Asabar don kaddamar da ofishin yakin neman zaben, ya nemi goyon bayan Omatseye Nesiama, dan takarar Sanatan Delta ta Kudu na jam’iyyar.

Dandazon al’umma ne dai su ka yi cikar kwari domin tarbar ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyar NNPP mai kayan marmari.

Kwankwaso ya bayyana cewa ba a fara yakin neman zabe a hukumance ba.

Ya ce dimbin jama’ar jam’iyyar da suka yi masa maraba a Warri sun tabbatar da farin jinin Nesiama da jam’iyyar a jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, ya ruwaito cewa Mista Nesiama da wasu amintattun jam’iyyar sun tarbe Kwankwaso da tawagarsa a filin jirgin sama na Osubi da ke karamar hukumar Okpe.

Kafin saukar Kwankwaso, magoya bayan jam’iyyar da dama ne su ka ajiye ayyukan su domin yin tattakin goyon baya ma jam’iyyar NNPP mai taken “Hope Walk” a ranar Asabar.

Kungiyar Kamfen din Nesiama ce ta shirya wannan tattakin na goyon baya, a wani ɓangare na shirye-shirye da aka tsara domin zuwan Kwankwaso da kuma kaddamar da ofishin Sanatan Delta ta Kudu na Commodore Nesiama.