
Dauda Lawan Dare a jiya Juma’a ya sake samun tikitin takarar gwamna a jam’iyyar PDP, a Zamfara a 2023.
An sake zaben Mista Lawan Dare ne da kuri’u 422 a zaben-fidda gwani da wata babbar kotun tarayya da ke Gusau ta bayar da umarnin a yi.
Shugaban kwamitin zaben-fidda gwani na gwamna na jam’iyyar PDP, kuma shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna, Hassan Hyet ne ya bayyana haka a karshen taron da aka gudanar a Gusau.
Hyet ya ce Lawan-Dare ya samu kuri’u 422 inda ya doke abokan hamayyarsa biyu da suka samu kuri’u ɗaya-ɗaya.
A cewarsa, daga cikin wakilai 431 da aka amince da su, 428 ne suka kaɗa kuri’ar inda ƙuri’u huɗu aka bayyana ba su da inganci.
Ya ce Dauda Lawan-Dare ya samu kuri’u 422, Ibrahim Shehu da Hafiz Nuhuche suka samu kuri’u ɗaya-ɗaya.
Ya ce: “Dr. Dauda Lawan-Dare, wanda ya samu kuri’u mafi yawa, an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa a jihar Zamfara.”
Hyet ya yi nuni da cewa ɗaya daga cikin ƴan takarar Wadatau Madawaki ya janye daga takarar kafin a fara zaben.