Home Labarai Mutane 4 sun rasu, an ceto 1 a ginin da ya rushe a Legas

Mutane 4 sun rasu, an ceto 1 a ginin da ya rushe a Legas

0
Mutane 4 sun rasu, an ceto 1 a ginin da ya rushe a Legas

 

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa, NEMA, a jiya Juma’a ta ce mutane huɗu ne su ka mutu yayin da aka ceto mutum ɗaya a rushewa ginin da ya faru a titin Oye Sonuga, Palm Avenue, a Mushin, Legas.

Ko’odinetan hukumar NEMA, shiyyar Kudu maso Yamma Ibrahim Farinloye ne ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a wata tattaunawa ta wayar tarho.

Ya ce maza biyu da mata biyu sun mutu, yayin da aka ceto mutum ɗaya a ruftawar ginin.

Tun da farko dai gwamnatin jihar Legas ta kuma ce za ta binciki musabbabin rugujewar ginin.

Kwamishinan tsare-tsare da raya birane, Omotayo Bamgbose-Martins ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Yayin da ya ziyarci wurin ginin benen mai hawa uku, wanda aka ce ya kai kimanin shekaru 40, ya ba da umarnin a rusa ginin nan take saboda dalilai na tsaro da kuma dakile kara rugujewar ginin.

Ya kuma umarci hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas, LASBCA, da dakin gwaje-gwajen kayyayakin gini ta jihar Legas da su bankaɗo musabbabin faduwar jirgin.