
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama wasu mutane biyu a jihar Kwara, bisa laifin safarar kwalabe 19,878 na wani sabon sinadarin sa maye, mai suna Akuskura.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa shi dai Akuskura wani sabon sindari ne da ake haɗa shi ya yi ƙarfi, inda ake kuskura wa, wani lokacin ma a na sha.
Idan a ka kuskura, ya kan baiwa mutum wani yanayi da har sai wanda ya yi ya fita daga hayyacinsa, wani lokacin har da kashi, amai da ma sumewa.
Sai dai kuma NDLEA ta cafke wadanda ake zargin, Oladokun Oluwaseun mai shekaru 49 da Ibrahim Jimoh mai shekaru 27, a kan babbar hanyar Ilorin zuwa Jebba a ranar Laraba, 21 ga watan Satumba.
Sun yi ikirarin cewa an yi lodin kayan ne a cikin manyan buhuhuna 35 a garin Ibadan na jihar Oyo, wanda aka yi nufin rabawa a garin Jos na jihar Plateau.
Hakazalika Jami’an hukumar NDLEA sun kama wani tsoho mai shekaru 75 mai suna Usman Bokina Bajama (wanda aka fi sani da Clemen) bisa laifin noman tabar wiwi.
An kama shi ne da sanyin safiyar ranar Talata, 20 ga watan Satumba a unguwar Anguwan Sate, Mararraban Tola, a yankin karamar hukumar Mayo Belwa a jihar Adamawa, inda ya ke da gonar tabar wiwi inda aka kwato kilogiram 49 na haramun.