
Daya daga cikin manyan sarakunan Najeriya, Maigari na Lokoja, Alhaji (Dr) Muhammad Kabir Maikarfi lll ya rasu.
Maigari, mai shekaru 80, ya rasu da yammacin jiya Laraba bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja.
Ya kasance ɗaya daga cikin sarakunan gargajiya mafi dad6ewa a jihar Kogi, inda ya hau karagar mulki a 1992.
Sakataren Majalisar Gargajiya na karamar hukumar Lokoja, Muhammed Nalado Usman ya tabbatar da rasuwar basaraken a wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Laraba.
Sanarwar ta ce za a yi jana’izar marigayin a yau Alhamis a Lokoja da karfe 4 na yamma.