
Wasu ƴan gida ɗaya su hudu sun mutu bayan sun ci amala, wani shahararren abincin a Nijeriya, a karamar hukumar Mopa Muro da ke jihar Kogi.
An bayyana cewa, wani mutum mai suna Pa Motilewa, matarsa, ƴaƴansa mata biyu da wata yarinya ƴar uwa gare su, sun girka amalar ne daga wani ragowar rogo da suka yi amfani da shi wajen yin fufu.
Wata majiya ta ce bayan sun kammala cin abincin ne sai su ka kamu da rashin lafiya, inda a ka yi kokarin duba lafiyarsu.
Sai dai kuma an ce ɗan auta a gidan ne ya fara rasuwa, inda ya rasu a ranar Juma’a, sai ɗan uwansa, yayin da wasu kuma aka garzaya da su asibitin ECWA da ke Egbe.
Sai dai babbar ‘ya’yan mata, mai suna Motun ta rasu ranar Lahadi, yayin da mahaifin ya rasu a ranar shima.
Mahaifiyar mai suna Molomo, an ce tana raye kuma ana sa ido sosai a kan lafiyarta.
Har yanzu ba a bayyana ko mutuwarsu na da nasaba da cin amalar ba.
A halin da ake ciki, kwamishinan yada labarai na Kogi, Kingsley Fanwo, a jiya Litinin, ya kai ziyarar jaje a fadar Elulu na Mopa a madadin gwamnan jihar, Yahaya Bello.
Ya ce gwamnan ya yi alhinin faruwar lamarin kuma “za a gudanar da bincike mai zurfi don gano musabbabin rasuwar ta su.
“Na zo nan ne domin mika ta’aziyyar gwamna, mai girma Yahaya Bello, ga Elulu in Council, HRH Oba Julius Joledo, JP, shugaban majalisar gargajiya na karamar hukumar Mopamuro, da daukacin al’ummar Mopa bisa rasuwar mutum hudu bayan cin abinci. Lamarin abin bakin ciki ne, mummuna da ban tsoro,” inji shi.
“Gwamnan ya umurci hukumomin tsaro da lafiya da su bincika su gano musabbabin lamarin.
“Ina so in tabbatar wa mai martaba cewa za a bayyana rahotan bincikensu a bainar jama’a kuma a dauki matakan da suka dace.”