Home Kanun Labarai DA ƊUMI-ƊUMI: APC ta sanya ranar fara gangamin yaƙin zaɓen shugaban ƙasa

DA ƊUMI-ƊUMI: APC ta sanya ranar fara gangamin yaƙin zaɓen shugaban ƙasa

0
DA ƊUMI-ƊUMI: APC ta sanya ranar fara gangamin yaƙin zaɓen shugaban ƙasa

 

 

 

Jam’iyyar APC mai mulki, za ta kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na 2023 a hukumance a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba, kamar yadda jaridar Vanguard ta jiyo.

Wannan ci gaban dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar da majalisar yakin neman zabenta ke shirin karbar dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ke da da dawo wa kasar.

Vanguard ta bayar da rahoto na musamman a yau Talata cewa ana sa ran Tinubu, wanda ya yi kwanaki a Landan zai dawo Najeriya cikin makon nan.