Home Lafiya Nijeriya na fuskantar haɗarin Ebola sakamakon ɓarkewar ta a Uganda

Nijeriya na fuskantar haɗarin Ebola sakamakon ɓarkewar ta a Uganda

0
Nijeriya na fuskantar haɗarin Ebola sakamakon ɓarkewar ta a Uganda

 

 

Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Ƙasa, NCDC ta ce Nijeriya na cikin haɗarin ɓullar cutar Ebola sakamakon ɓarkewar ta a ƙasar Uganda.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta NCDC ta fitar a a jiya Talata, mai dauke da sa hannun babban daraktan ta, Dr Ifedayo Adetifa, ta bayyana cewa tana cikin shirin ko-ta-kwana, inda ta kara da cewa “yiwuwar shigo da cutar zuwa Najeriya ya yi yawa saboda karuwar zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Najeriya da Uganda, musamman ta filin jirgin saman Nairobi na Kenya, cibiyar sufurin jiragen ruwa, da sauran kasashe makwabta da ke da iyaka da Uganda.”

A cewar NCDC, cutar Ebola da ke ci gaba da yaɗuwa ta samo asali ne daga nau’in cutar Ebola na Sudan a Uganda kamar yadda aka ayyana a ranar 20 ga Satumba, 2022.