
Sama da ɗalibai 300 na Cibiyar Koyar da Sana’o’i ta Zamani ta Dangote, da su ka haɗa da fiye da rabin adadin wadanda aka horas, sun yi kukan an kore su daga cibiyar.
Ɗaliban, waɗanda su ka fito wata gaggarumar zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira dakatar da horon da aka yi musu ba bisa ka’ida ba, ba tare da bin ka’ida ba, sun kasance a fadar gwamnatin Kano da fadar sarakin Kano a jihar, inda su ke zargin babban daraktan cibiyar, Paul Quin da hannu a korar ta su.
Zanga-zangar, ƙarƙashin jagorancin daya daga cikin daliban da aka kora, Abubakar Isma’il DTurawa ta nemi hukumomin da abin ya shafa da su sa baki domin mayar da su makarantar.
“Muna rokon gwamnati da ta sa baki ta dawo da mu cibiyar mu domin mu kammala horon da a ke mana da kuma amfana daga dukkan shirye-shiryen da aka shirya mana,” in ji shi.
Kokarin tattaunawa da Daraktan ya ci tura domin bai amsa kiran nasa ba ko kuma amsa sakon da aka aika masa.
Daily Trust