Home Siyasa PDP ta musanta bai wa manyan shugabanninta cin hanci

PDP ta musanta bai wa manyan shugabanninta cin hanci

0
PDP ta musanta bai wa manyan shugabanninta cin hanci

 

 

 

Kwamitin gudanarwar babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya, ya musanta rahotonni da ke cewa an bai wa wasu manyan jagororin jam’iyyar cin hanci.

Kwamitin ya ce kudaden alawus din gidaje ne wanda aka aiwatar bisa tsarin doka, ba cin hanci ba kamar yadda ake zargi.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar Debo Ologunagba ya fitar ranar Talata bayan kammala taron kwamitin zartarwar jam’iyyar a Abuja babban birnin kasar.

Ologunagba ya ce a zaman da kwamitin ya yi, ya yi duba game da labarin da wata jarida a kasar ta buga, tana mai cewa kudin alawus din gidaje da aka biya manyan jagororin jam’iyyar kudi ne na cin hanci.

“Bayan bincike da kwamitin ya gudanar a zamansa, ya fahimci cewa kudin ba cin hanci ba, kudin alawus din gidaje ne,” in ji shi.

Ologunagba ya ce jam’iyyar ta kafa kwamiti tare da ba shi wa’adin mako guda domin duba lamarin tare da mika rahotonsa ga kwamitin gudanarwar jam’iyyar domin daukar mataki na gaba.