Home Siyasa 2023: Obi zai baiwa ƴan Nijeriya mamaki, in ji ɗan takarar gwamnan Kano na LP

2023: Obi zai baiwa ƴan Nijeriya mamaki, in ji ɗan takarar gwamnan Kano na LP

0
2023: Obi zai baiwa ƴan Nijeriya mamaki, in ji ɗan takarar gwamnan Kano na LP

 

 

 

Dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour Party (LP) a jihar Kano, Injiniya Bashir Ishaq Bashir, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi zai baiwa ƴan Najeriya mamaki idan ya lashe zaɓen 2023.

Injiniya Bashir ya bayyana haka ne a yayin taron tattaunawa na 2023, wanda kungiyar wakilan gidajen jaridu, reshen jihar Kano ta shirya a ranar Juma’a.

Injiniys Bashir ya kuma ce kamar Obi, shi ma zai ba da mamaki idan ya ci zaben gwamna a jihar Kano.

A cewarsa, yanzu mutane sun fi sha’awar nagartar ɗan takara, ba jam’iyyar siyasa ba, ya kara da cewa ya kamata jam’iyyun APC da PDP su daina mafarkin cin zabe domin jama’a sun gaji da gazawarsu a wa’adin mulkinsu.

Ya ce Obi da shi suna da abin da ya kamata su ci zabe, yana mai cewa jam’iyyarsa ta Labour ce ke da manufa mafi kyau ga ƴan Nijeriya.